Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta amince da kawo sabbin kwasa kwasan digiri guda biyar a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Bauch

Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta amince kawo digiri akan kwasa-kwasai guda biyar da za a gudanar a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Bauchi, a haɗaka da Jami’ar Maiduguri (UNIMAID).

Sabbin kwasa-kwasan sun hada da Bsc Mass Communication, Bsc Accounting, Bsc Business Administration, Bsc Banking and Finance da kuma Bsc Public Administration.

KARANTA WANNAN: Kasuwar Ibadan Ta Kama Da Wuta

Hukumar NUC ta bayar da wannan amincewa ne bayan ziyarar tantancewar masana domin duba ƙwarewa tare da kayan aiki da aka tanadar don neman izinin fara wadan nan Sabbin kwasa-kwasai.

Kwalejin ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Haka kuma, ta ƙara da cewa za a fara karɓar dalibai daga shekarar karatun 2024/2025.

A tuna cewa Kwalejin tana gudanar da digiri a fannonin injiniyanci ta hanyar haɗaka da Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi (ATBU).