Kayayyakin al’umma da kadarorin miliyoyin nera ne su ka kone yayin da iftila’in gobara ya afkawa babbar kasuwar Araromi da ke Agodi-Gate, a babban birnin badan na jihar Oyo.
Ance gobarar ta fa ra ne da misalin karfe 2 na safiyar ranar Asabar, kuma ta na ci gaba da ruruwa, inda jami’an kashe gobara na jihar Oyo ke kokarin shawo kan lamarin.
Janar Manajan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Oyo, Akinyemi Akinyinka, ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Asabar, inda ya bayyana lamarin a matsayin mawuyacin hali.
Kazalika, har ya zuwa yanzu ba’a gano abin da ya haddasa gobarar ba.