Ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, ya kwace filayen jiga-jigan ‘yan siyasar Najeriya, ciki har da na gidauniyar tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari, da tsohon Babban Mai Shari’ar Nigeria, Walter Onnoghen, da Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas da kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume da na matarsa; Regina, tare kuma da na Gwamnan Kaduna, Uba Sani.
Wike, ya kwace filaye 762 a yankin Maitama sakamako waɗan da abin ya shafa sun ki biyan kudaden takardar mallaka filayen bisa ka’ida.
Nyeson Wike, ya ce ya yanke shawarar daukar matakin ne karkashin sashin dokar filaye ta 28 wacce ta sahale wa Ministan Abuja damar kwace filaye bisa rashin biyan kudaden da kodar ta tanada ko kuma bisa karya wasu ka’idoji.
Kazalika, Ministan Abujan, ya kuma yi barazanar kwace wasu karin filayen guda 614 na wasu mutane da kuma kamfanoni matuƙar basu biya kuɗaɗen shaidar mallakar su ba nan da makwanni biyu.
Fassara: Shamsuddeen Alhaji Musa